Habasha ta ce 'yan kasarta kungiyar IS ta kashe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar IS ta kashe 'yan ciranin Ethiopia.

Kasar Habasha ta tabbatar da cewa mutanen da aka nuna yadda aka kashesu a wani bidiyo da kungiyar IS ta fitar a ranar Lahadi 'yan kasarta ne da su ka tafi ci rani.

Gwamnatin Habasha ta sanya kwana uku domin ayi jimamin mutuwar mutanen ta kuma ce ta na iyakar kokari don gano sunayensu.

A cikin bidiyon an nuna yadda aka harbi fiye da mutane 20 a kansu yayin da aka fille kawunan wadansu.

Alamun da aka gani a bidiyon na nuna cewa an kashe mutanen ne saboda kasancewarsu kiristoci.

Ana zargin a Libya al'amarin ya faru.

Gwamnatin Amurka da Tarayyar Turai EU, sun kyamaci wannan kisa.