Bam ya fashe a Potiskum

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan shi'a da 'yan Boko Haram suka kashe a shekarar 2015

Rahotanni daga garin Potiskum a jihar Yobe da ke Nigeria na cewa wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a makarantar mabiya Shi'a da ke garin.

Wadanda al'amarin ya faru a gabansu sun shaida wa BBC cewa dan kunar bakin waken ya zo ne da zummar shiga makarantar sai bam din ya tashi.

Ba a samu hasarar rayuka ba sai na dan kunar bakin waken, yayin kimanin mutane shida kuma su ka jikkata.

Garin Potiskum ya kasance daya daga cikin garuruwan da 'yan Boko Haram suka sha kaddamar da hare-hare a cikin 'yan shekarun nan.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Nigeria tare da raba wasu mutanen da muhallansu.