'Yan PDP da APC na ta da jijiyar wuya a Taraba

Image caption A rabar Asabar za a sake gudanar da zabe a wasu mazabu na jihar Taraba

A dai-dai lokacin da ya rage kwanaki biyar a sake gudanar da zaben gwamna a wasu mazabu na jihar Taraba, magoya bayan jam'iyyun biyu na ci gaba da tayar da jijiyar wuya dangane da kiki-kakar data kai ga soke zaben a wadannan mazabu tun da farko.

Kowane bangare dai na zargin dayan da kokarin tafka magudin da ya kai hukumar zabe soke zabukan wadannan mazabun, bayan ganin cewa dan- takarar daya bangaren ya kama hanyar lashe zaben.

Eric Yohana Ikino dan Taraba Volunteer Group dake goyon bayan dan takarar jam'iyyar PDP ya shaida wa BBC cewa ba a shirya wa jam'iyyarsa gaskiya ba.

"A karamar hukumuta ta Donga an kashe zaben gaba daya an ce wai akwai rikici a mazabu guda biyar, to idan gaskiya ne me ya sa ba za a soke na mazabu biyar din ba a bar ragowar 160 din?" in ji Mr Ikino.

Shi kuwa Alhaji Hassan Jikan Haro, shugaban jam'iyar APC a jihar Taraba cewa ya yi "A karamar hukumar Wukari akwai mazabu 56 a yankin Bantaje, amma da aka tashi kai akwatunan zabe sai aka kai 11 kacal sai su ka hada baki su ka ringizo kuri'u."

A ranar 25 ga watan Afrilu ne dai za a sake gudanar da zaben a wasu mazabu na jihar Taraba tsakanin dan takarar jam'iyyar PDP Mr. Darius Ishaku da kuma Sanata Aisha Jummai Alhassan ta jam'iyyar APC.