'Yan shi'a a Yemen na zargin Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin 'yan tawayen Yemen da sojojin gwamnati

Magunguna da kuma kayayyakin aiki na karewa a asibitocin birnin Aden mai tashar jiragen ruwa a Yemen yayinda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun Gwamnati dake samun goyan bayan gamayyar sojojin dake karkashin jagorancin Saudiyya da kuma mayakan Houthi.

An fadawa wata mai aiko da BBC rahotanni da ta ziyarci birnin cewa marasa lafiyar da aka kwantar na mutuwa saboda ba za a iya basu cikakkiyar kulawa ba ,saboda rashin kayan aikin da kuma magunguna.

Wakiliyar BBC ta kara da cewa yayin ziyarar tasu zuwa asibitin babu wutar lantarki, sannan kuma babu mai a cikin janaretan asibitin.

Kowacce rana kuma ana samun marasa lafiya sabbi har 30 da suke tudada asibitin sakamakon harbin bindiga

Jagoran 'yan tawayen Houthin dai ya zargi Kasar Saudiyya da kokarin mamaye kasar, yayinda daruruwan mutane ke mutuwa sakamakon luguden boma bomai