Sarkin Zulu na neman sulhu a Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarkin gargajia na kabilar Zulu, Goodwill Zwelithini.

Sarkin gargajiya na kabilar Zulu a Afrika ta Kudu, Goodwill Zwelithini, ya shirya muhawara da wasu sarakunan domin a nemi hanyar kwantar wa 'yan ci-rani hankula dangane da hare-haren da aka kai masu a KwaZulu-Natal.

Mutane da dama da sun dora laifin hare-haren a kan sarkin inda suka ce furucin sa na makonni uku da suka wuce su ne musabbabin rikicin, duk da dai ya ce ba a fahimce manufar sa bane.

An tilasta wa sarkin da ya sa baki domin a samu maslaha ga wannan fitina da ta janyo mutuwar mutane shida.

'Yan sandan Afrika ta Kudu sun kama mutane fiye da 300 da suke zargin suna da hannu a kashe-kashe da kone-konen da suka auku a garin.

Matasa bakar fata 'yan Afrika ta Kudu sun kadammar da hare-hare a kan baki 'yan wasu kasashen Afrika.