Amurka ta musantan zargin Iran

Hakkin mallakar hoto WP
Image caption Jason Rezaian, mai kawo rahotannin jaridar Washington Post.

Gwamnatin Amurka ta ce babu kanshin gaskiya game da zarge- zargen leken asirin da ake yi wa mai aikowa da Washington Post rahotanni daga Iran.

Ana zargin Jason Rezaian da hada kai tare da wasu kasashen da ba sa shiri da Iran domin yada farfaganda game da ita.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce Washington ba ta sami wani tabbaci ba a hukumace ba na zarge zargen, amma ta yi kiran da a saki dan jaridar Mr Rezaian nan take.

An dai tsare shi ne a Tehran watanni tara da suka gabata.

Kuma lauyarsa ta ce masu gabatar da kara basu gabatar da wata hujja ba da ke gaskata zarge zargen da ake masa, wadanda tace nada alaka da aikinsa na dan-jarida.