EU ta dauki mataki a kan mutuwar 'yan cirani

Hakkin mallakar hoto b
Image caption 'Yan ci rani zuwa kasashen Turai

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana wani tsari mai matakai 10 domin magance mutuwar 'yan ci rani a lokacin da suke ketara tekuin Bahar Rum.

Tsarin zai hada da kara karfafa aikin bincike da ceto a tekun, sannan za a bullo da wata dabara ta lalata kwale-kwalen da masu fataucin mutane ke amfani da su.

Za kuma a dauki matakai na rage kwararar 'yan ci rani da kuma bullo da hanyoyin mayar da wadanda suka samu shiga Turai kasashen su.

A ranar Alhamis ne shugabannin Tarayyar Turan zasu tattauna wannan tsari.

A hannu huda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana fargabar mutane 800 ne suka mutu lokacin da jirgin ruwan da ke dauke da 'yan ci rani ya kife a tekun na Bahar Rum a ranar Lahadi.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ta yi magana da wasu daga cikin mutane 28 da suka samu tsira daga hadarin bayan sun samu isa tashar jiragen ruwa ta Sicily da ke Catania.

Fasinjojin da suke cikin jirgin sun fito ne daga kasashe da dama, da suka hada da Eritrea da Somalia da Syria da wasu kasashen yammacin Afrika fiye da shida.

'Yan sandan Italiya sun kama mutane biyu daga cikin 28 din da aka ceto bisa zarginsu da taimaka wa ayi fataucin mutane.