An soma makokin kwanaki 3 a Habasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan IS sun kashe Kiristocin Habasha a Libya

A ranar TAlata ne aka fara makokin kwanaki uku a kasar Habasha domin alhinin mutuwar 'yan kasar da mayakan IS suka kashe a Libya.

An yi kasa kasa da Tutocin kasar, sannan majalisar dokokin kasar za ta yi wani zama domin tattauna martanin da kasar zata mayar game da kisan gillar da aka yi wa 'yan kasar fiye da 20.

Wani kakakin gwamnatin Habashan yace anyi imanin cewar mutanen da aka kashe din 'yan cirani ne wadanda ke kokarin shiga nahiyar Turai daga Libya.

Kungiyar Tarayyar Afirka wacce ke da hedikwata a Habasha ta yi Allah-wadai da isan sannan tana yin aiki domin dawo da tsaro a Libya.

A ranar Lahadi ne mayakan dake ikirarin yin jihadin suka fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda su ka kashe Kiristocin Habashan.