An yi kiran kaurace wa kayan Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Afrika ta Kudun na ganin baki sun mamaye musu harkokin kasuwanci

A biranen Najeriya daban-daban ana ci gaba da zanga-zangar mayar da martani kan tarzomar kyamar baki 'yan kasashen Afrika da wasu ke yi a Afrika ta Kudu.

A Kaduna da Enugu, an yi zanga-zangar neman goyon bayan sauran 'yan Najeriyar domin mayar da martani kan Afrika ta Kudun.

Masu zanga zangar sun nemi da a kaurace wa kayayyakin kamfanonin Afrika ta Kudu, irin su MTN da DSTV da Shoprite da sauransu.

Masu lura da al'amura na ganin abin da ke faruwa a Afrika ta Kudun butulci ne ga sauran 'yan Afrika da duniya.

Suna ganin Najeriya da sauran kasashen Afrika da na duniya sun kashe kudade tare da taimaka wa Afrika ta Kudu wajen samun 'yanci daga Turawa masu wariyar launin fata.