Za a tura dakaru zuwa birnin Johannesburg

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Afrika ta kudu na ci gaba da kin jinin baki

Ministar tsaron Afrika ta Kudu, Nosiviwe Mapisa-Nqakula, ta sanar da cewa za a kai sojoji cikin birnin Alexandra da ke Johannesburg a yayin da rikici ke kara kamari kan kin jinin baki da 'yan kasar ke yi.

Kawo yanzu lamarin ya jawo mutuwar mutane bakwai.

Ministar ta ce an kashe wasu ma'aurata 'yan kasar Zimbabwe a cikin birnin, a ranar Litinin da daddare.

An kuma kashe wani dan kasar Mozambik a wannan yankin a ranar Asabar.

Tun a ranar 15 ga watan Afrilu ne aka soma rikici a kasar sakamakon zargin da 'yan kasar Afrika ta Kudu suka yi cewa baki sun kwace dukkanin ayyukan da suka kamata a ba su.

A yanzu haka kashi 24 cikin 100 na 'yan Afrika ta Kudu ba su da aikin yi.