Jirgin yakin Saudiyya ya hallaka 'yan Yemen

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Saudiyya ta kai harin jirgin sama a Yemen.

Rahotanni daga Yemen sun ce an kashe akalla mutane 29 a wani harin jirgin sama da kasar Saudiyya ta kai wa mayakan 'yan Houthi.

Wani hari da aka kai ya tarwatsa taron da mayakan ke yi a garin Ibb da ke yammacin kasar.

An samu wasu rahotanni masu cin karo da juna na adadin mutanen da aka kashe tsakanin 'yan tawayen 'yan shi'a da kuma na fararen hula.

An kuma kai hari wani gini a birnin Haradh, wanda ke kusa da Saudiyya.