An zargi gwamnatin Yobe da kama malamin addini

Hakkin mallakar hoto yobe govt

A jihar Yobe dake arewa maso gabashin Nigeria, iyalin wani malamin addinin musulunci sun zargi gwamnatin Jihar da kama malamin da kuma ci gaba da tsare shi.

Iyalin Malam Abubakar Ciroma sun yi zargin cewa gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan wa'azin da Malamin ya yi jajiberin zaben gwamnoni inda ya yi kira ga mutanen jihar da cewa kada su sake zabar Gwamna Ibrahim Gaidam.

Daya daga cikin matan Malamin ta fadawa BBC cewa tun bayan da aka tsare shi, ba su sake jin duriyarsa ba, kuma har yanzu ba su ganshi ba.

Iyalin malamin dai sun ce suna cikin damuwa.

Sai dai kakakin gwamnan Jihar Yobe ya ce gwamnatin jiha bata da masaniya game da kama malamin

Abdullahi Bego ya ce jami'an tsaro ne kawai za su iya yin bayani game da kama malamin