“Libya na da matukar hadari” inji Dan Ci-rani

Hakkin mallakar hoto Getty images

Kungiyar Tarayyar Turai ta dauki matakai domin saukaka wahalhalun da ‘yan cirani ke fuskanta a tekun Bahar Rum inda a ‘yan kwanakin da suka gabata kawai daruruwan mutane suka rasa rayukansu.

A nan, wani dan ci-ranin Afrika mai suna Gassama ne ya bayyana yadda tafiyarsa ta kasance daga kasar Gambiya zuwa Turai inda ya ratsa ta Libya, da kuma yadda a yanzu yake son raunana gwiwar masu burin gudun hijira da kada su yi wannan tafiya mai cike da kasada.

“A watan Nuwambar bara ne na samu tsallake Libya zuwa Sicily, bayan na sha gwada haka din ba tare da nasara ba.

Ni dan kasar Gambiya ne kuma tun a shekarar 2009 na bar kasata da zummar zuwa Turai.

A tafiyar tawa kuma na bi ta kasashe kamar Senegal da Mali har zuwa Libiya, kuma duk inda na samu sararin yin aikin karfi nakan yi domin in tara kudin tafiya.

Na yi ayyuka kamar lodin kaya a babbar mota da duk wani aiki ma da ya zo hannuna.

Daga karshe dai na samu isa Libya cikin matukar galabaita.

Image caption Gassama ya bude wannan zaure a shafin Facebook domin ya raunana gwiwar 'yan uwansa 'yan ci rani masu niyyar zuwa Turai ta Libya

Akwai wahalar samun aiki a Libya. Sau uku ana kamani an kuma kai bni gidan yari daban-daban har guda biyar.

Kuma a duk lokacin da aka kai ni gidan yari sai na biya kudi kafin a sake ni.

Sannan kuma na biya mutane daban-daban kudi duk a kokarin ganin na samu shiga jirgin ruwan da zai tsallaka da ni zuwa Italiya.

Mutanen da ke kula da wadannan jiragen ruwa suna karbar kudin mutane kuma sai su loda mutane da yawa a jiragen.

Da wuya kuma mutum ya samu shiga jirgin saboda turereniya, su dai za su karbi kudinka ta kowanne hali.

Ban yi nasara ba a kokarin farko da na yi domin samun shiga jirgin.

Bayan mun shafe kwanaki biyu a cikin ruwa dole muka juyo.

A karshe dai na samu shiga wani jirgin inda na biya dala 870, bayan da wani wanda na sani ya taimaka min na sami kudin.

Akwai mutane dankam a cikin jirgin kuma babu wata cikakkiyar kariya. Bayan doguwar tafiya mai tsananin wahala, a karshe dai na samu isa Sicily a galabaice.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An tseratar da 'yan ci-rani da dama a Libya da Turai, bayan sun yi tafiy-tafiye masu cike da hatsari

Daga nan ne kuma, na karaso Milan.

Al’amuran dai ba sauki ko kadan saboda na fuskanci kyara da sauran matsaloli, amma dai na yi farin ciki da na samu tsallakewa.

Tuntuni na bude wani zaure a shafin Facebook inda nake kokarin wayar da kan mutane masu kokarin bi ta Libya domin su tsallaka Turai su san irin tsananin wahalar da ke kunshe cikin bulaguron.

Na yi Magana da mutane da dama wadanda suka tuntubeni ta shafin Facebook dina kuma I zuwa yanzu na samu kyakkyawan hadin kansu.

Na yi kokarin gamsar da su da kada su yi kasadar biyowa ta Libiya saboda tana da matukar hatsari, kuma zan ci gaba da gaya musu gaskiya.

Suna da dukkan damar da za su yi kokarin zuwa Turai kamar yadda na yi, amma tafiya ta hanyar Libiya babban tashin hankali ne.

Al’amari ne da zai dagula maka lissafi kuma a yanzu ya zama mai matukar hatsari.

Akwai mutanen da za su yi kokarin yi maka fashi su kwace kudinka domin kawai ka samu shiga cikin jirgin ruwan nan wanda yake cike makil kuma babu wata kariya a tare da shi.

Wakilin BBC Stephen Fottrell ne ya yi hirar.