Amurka: Makafi sun yi karar kamfani a kan karnuka

Hakkin mallakar hoto BBC EARTH
Image caption Makafi sun kai karar kamfani saboda kin yarda ya dauki karnukansu

Kungiyar makafi ta Amurka da ke California ta yi karar kamfanin hayar motoci na Uber bisa nuna wariya ga masu nakasa ta rashin gani.

'Yan kungiyar dai suna karar kamfanin ne saboda kin daukar karnukansu da suke yi musu jagora da direbobin kamfanin ke yi.

Sun zayyana laifuka har guda 40 da suke tuhumar kamfanin da su.

Daya daga laifukan da ake zargin kamfanin shi ne wasu direbobin kamfanin suna fada da karfi cewa ba ma daukar karnuka a motocinmu.

Haka kuma an taba samun wani direban kamfanin da laifin kin amincewa ya bude wa wata makahuwa kofa ta fita daga motar bayan da ta gano cewa an kulle mata karenta a akwatin motar, wato boot.

Sai dai kuma kamfanin ya ce ya ba wa direbobinsa umarnin daukar dabbobi masu alaka da mutane.

Saboda haka kungiyar ba ta da hurumin tuhumar kamfanin.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Makafi na yin amfani da karnuka a matsayin 'yan jagora a Amurka

Yanzu haka dai an saurari karar kuma an ba wa kamfanin na Uber har zuwa 2 ga watan Mayu da ya mayar da martani dangane da tuhumar da ake yi masa.