"Na tako daga Lagos zuwa Abuja saboda Buhari"

Image caption Cincinrindon mutanen da suka tarbi Sulaiman Hashimu a Abuja

Matashi nan dan Najeriya, Sulaiman Hashimu, wanda ya yi tattaki daga Lagos zuwa Abuja babban birnin tarayya a kasa, ya ce ya ga abubuwa da dama daga cikin matsalolin da 'yan Najeriya ke fuskanta a rayuwa ta yau da kullum.

Shi dai wannan matashi ya yi wannan tafiya ne domin cika al'kawarin da ya yi na cewa idan Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa zai yi wannan tattaki a kasa.

Sulaiman ya shaida wa BBC cewa ya ga al'amura da yawa a wannan tafiya da ya yi, yana mai cewa: "Wallahi akwai mutanen Nigeria da gwamnati sam ba ta mu'amala da su, na ga mutane cikin wahala da bakin talauci da ya kamata a tallafa musu."

Ya kara da cewa tafiya mabudin ilimi ce "na fahimci cewa wannan rayuwa mai sauki ce domin haka ya kamata mutane su dinga kulla gaskiya a dukkan lamari."

Malam Sulaiman ya kuma yi kira ga 'yan siyasa da su dinga kamanta adalci ga talakawan suke zabarsu da nuna musu soyayya.

Sulaiman ya ce ya ratsa manyan garuruwa a tafiyarsa ta kwanaki 18, kamar su Jaba da Oyo da Ogbomosho da Ilori da Bodar Sa'adu da Jaba da Mokwa da Kutigi da Bidda da Suleja har ya dangana da Abuja.

A cewarsa, "A kiyasin da jami'an tsaro dai suka yi sunce na kan yi tafiyar kilomita 70 a duk rana."

Sulaiman Hashimu -- mai shekaru 33 -- dan asalin garin Funtuwa ne da ke jihar Katsina amma ya girma a jihar Oyo.