Gwamnatin India ta rufe tashar Al-Jazeera

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An toshe tashar Al-Jazeera a India.

Gwamnatin India ta dakatar da tashar talbijin ta Al-Jazeera daga watsa shire-shiryenta na tsawon kwanaki 5, sakamakon taswirar yankin Kashmir da tashar ta nuna ba dai-dai ba.

Tun bayan rufe tashar dai jama'a basa iya kallonta, sai dai su ga sakon da ke sanar da cewa ba za a bude ta ba sai 27 ga watan Afrilu.

Wani kwamitin gwamnatin kasar ya bayyana abin da Al-Jazeeran ta yi a matsayin cin fuska kan yadda ta nuna a taswirar cewa yankin Kashmir ya rabu ne tsakanin India da Pakistan da kuma China.

Har yanzu dai ba a tabbatar da matsayin yankin Kashmir ba a dokar kasa da kasa.

Gwamnatin India tana sa ido a kan yadda kafofin yada labarai akai-akai kan duk abin da ya shafi yankunanta.