Boko Haram ta sauya sunanta

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Sabobbin hotunan 'yan Boko Haram

Kungiyar Boko Haram ta fitar da sababbin hotunan mayakanta, wanda a cikinsa, ta sauya suna daga Jama'atu Ahlussunnah Lidda'awati wal Jihad zuwa daular Musulunci da ke yammacin Afrika.

Hotunan sun nuna mayakan kungiyar -- wadanda ta ce daga bisa ni an kashe su a fafatawa da jami'an tsaro.

Hotunan, wadanda aka wallafa a shafukan zumunta na zamani, an bayyana mayakan a matsayin wadanda suka yi shahada.

Sabanin yadda kungiyar Boko Haram ta saba fitar da hotunanta a baya, a wannan karon mayakan kungiyar ba su rufe fuskokinsa ba.

A cikin watan Maris ne shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi mubaya'a ga kungiyar IS.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan dakarun Nigeria sun ce sun kaddamar da hare-hare a dajin Sambisa, wurin da ake gani shi ne maboya ta karshe da kungiyar Boko Haram ke zama.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Boko Haram na cikin kungiyoyin 'yan ta'addan da suka fi kudi a duniya.

Ana zaton 'yan matan Chibok sama da 200 da kungiyar ta sace, suna rike da su ne a dajin Sambisa.