An gano maganin da zai iya warkar da Ebola

Image caption Masana kimiyya a ko'ina a fadin duniya sun sha fitar da magunguna daban-daban domin warkar da cutar Ebola

Masana kimiyya a Amurka sun ce wani maganin gwaji na cutar Ebola, ya ceci rayuwar wasu birrai uku da suka kamu da kwayar cutar kuma maganin zai iya aiki a kan mutane.

Masu binciken a jami'ar Texas, sun ce an sanya kwayar cutar ta Ebola a jikin birran, wadda ita ce sanadiyyar barkewar cutar a Yammacin Afrika.

Daga nan sai aka ba su magani, bayan kwana uku kuma suka rayu duk da tsananin zazzabi da yawan kwayar cutar a jikinsu.

Dr Alexander van Tullecan, kwararre a kan cutar ta Ebola, ya ce za a iya samar da maganin cikin makonni takwas kuma za a iya sarrafa shi domin maganin nau'in kwayar cutar daban-daban.

''Ina ganin abin sha'awa da wannan magani, shi ne za a iya amfani da shi a kan nau'in kwayar cutar ta Ebola daban-daban, saboda haka wannan gwajin, ba ya nuna cewa za mu iya amfani da maganin ko da kwayar cutar ta rikide ta sauya yanayi,'' a cewar Dr Tullecan.

Cutar Ebola dai ta hallaka mutane da dama a Afrika ta yamma musamman a kasashen Liberiya da Saliyo da Guinea.