EU na taron gaggawa kan 'yan cirani

Hakkin mallakar hoto Getty images
Image caption Tarayyar Turai tana taron gaggawa kan 'yan cirani

A yau Alhamis ne shugabannin kungiyar Tarayyar Turai suke yin wani taron gaggawa a Brussels domin lalubo hanyoyin takaita yadda bakin haure ke tururuwa zuwa Turai da kuma hadarin da suke fuskanta na ketare tekun Bahar Rum a wannan tafiya.

Kuma daya daga cikin abubuwan da ake ganin za a tattauna a kai shi ne yuwuwar ba wa sojoji damar lalata duk wani jirgin ruwa da masu fataucin mutane ke yin amfani da shi.

Sannan kuma za a tattauna yadda za a samar da tabbatacciyar gwamnati a Libya kasancewar kasar wata kafa ta ketarawa zuwa turai.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai sama da 'yan ciranin dari takwas suka halaka a tekun a yankin Libya.

Kawo yanzu an yi kiyasin wadanda suka mutu a tekun sun kai 1,750 a wannan shekarar.