Sankarau: Za a fara allurar rigakafi a Niger

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption shugaban kasar jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar za su fara yi wa yara riga-kafin cutar sankarau a gobe Juma'a.

Ranar Laraba ne dai aka rufe daukacin makarantun boko na birnin Yamai da kewaye domin yin riga-kafin.

Makarantun za su ci gaba da zama a rufe har zuwa ranar Litinin mai zuwa.

Sai dai hukumomin sun ce allurar riga-kafin miliyan daya da dubu dari biyu kawai suke da ita, wanda adadin shi ne rabin abin da ake bukata domin yi wa dukkan yara masu shekara biyu zuwa 15 riga-kafin.

Mutane kusan dari tara ne dai suka kamu da annobar ta sankarau a inda tayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 80 a shekarar nan ta 2015.