Amurka ta ji takaicin mutuwar 'yan kasarta

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaba Obama ya ce sun yi kuskure

Fadar White House ta Amurka ta bayyana cewa 'yan kasashen yamma biyu sun mutu a lokacin wani hari da jirgi marar matuki da aka kai a kan iyakar Afghanistan da Pakistan a watan Janairu.

Shugaba Obama ya ce ya ji matukar takaici a kan kuskuren da aka yi na kashe ma'aikatan agajin biyu-- Warren Weinstein wanda Ba'amurke ne da kuma dan Italiya Giovanni Lo Porto.

Kungiyar Alka'ida ta yi garkuwa da su na tsawon lokaci.

Shugaba Obama ya ce Amurka ba ta san cewar a cikin gidan aka boye Turawan ba a lokacin da ta kai hari.

A lokacin harin an kashe wasu Amurkawa biyu mambobin kungiyar Al-ka'ida.