Sabon fada ya barke a Ukraine

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Fada ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin 'Yan aware da sojoji a gabashin Ukraine

Rahotanni na cewa 'yan awaren da Rasha ke goyon baya suna ta yin luguden wuta a kan sansanonin dakarun sojin Ukraine da ke gabashin birnin Mariupol.

Wani wakilin BBC ya ga shaidar da ke nuna cewa an yi amfani da manyan makamai wanda hakan ya saba yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanya wa hannu a Minsk a watan Fabrairu.

Wakilin BBC ya kara da cewa an fara yin luguden wutar ne, jim kadan bayan wata tawagar masu sa ido ta kasashen duniya ta bar yankin.

An dai fara luguden wuta na baya-bayan nan ne yayin da Amurka ta zargi Rasha da samar da wata kariya ta sama daga hare-haren da za a iya kai mata a gabashin Ukraine.

Kazalika mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Marie Harf, ta zargi Rasha kan karin dakarun da ta tura zuwa yankin, amma Rashar ta musanta zargin.