Ba mu da laifi a kisan kiyashin 'yan Armenia —Turkiyya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan

Turkiyya ta musanta zargin da kasar Armenia da wasu kasashen duniya suke yi mata cewa ita ce take da laifin kashe Armeniyawa miliyan daya da rabi a shekarar 1915, lokacin yakin duniya na daya.

Turkiyya ta ce babu gaskiya a cikin batun kisan gillar domin dukkanin bangarorin sun rasa 'yan kasarsu a lokacin yakin, tana mai cewa sojojinta dubu 86 ne suka mutu.

A wannan yaki dai, kasar Turkiyya tana mara wa Jamus baya ne, yayin da ita kuma Armenia take tallafawa Rasha mai goyon bayan Biritaniya da Faransa.

A duk ranar 24 ga watan Aprilu, 'yan asalin kasar Armenia daga ko'ina a fadin duniya suna taron tunawa da wannan kisan, a babban birnin kasar, Yerevan.

A wannan karon, ana sa ran shugabannin kasashen da suka hada da Faransa da Rasha za su halarci wajen alhinin.