Cameron ne ke jawo hatsarin 'yan ci-rani - Ed Miliband

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jam'iyyar adawa ta zargi David Cameron da alhakin hatsarin 'yan ci ranin Afrika

Dan takarar jam'iyar Labour a Biritaniya, Ed Miliband, ya dora alhakin hatsarin da ake samu na 'yan ci ranin Afrika da ke tsallake tekun Bahar Rum zuwa Turai a kan Firai ministan kasar, David Cameron.

Mr Miliband ya yi zargin ne a wani jawabi da ake zaton zai gabatar a gaban jama'a a ranar Juma'a.

Ya kara da cewa hatsarin 'yan ci ranin na faruwa ne saboda juya bayan da Mr Cameron ya yi wa kasar Libya, sakamakon sanya bakin da kasashen duniya suka yi a rikicin kasar.

Mr Miliband ya kuma kalubalanci Mr Cameron din a kan abin da ya kira dauke-kai daga irin zaluncin da Rasha ke yi da mu'amalarsa da China da kuma sauye-sauyen fasalin tarayyar Turai, wanda hakan ya janyo zubewar kimar Biritaniya.

Tuni dai wani kakakin jam'iyyar Conservative mai mulki ya yi tur ga kalaman da ake zaton Mr Milibanda zai yi din, yana mai cewa "hakan babban abin kunya ne da zubar da kima."

Wannan takaddama dai tana zuwa ne yayin da ya rage makonni biyu a gudanar da babban zabe a Biritaniyan.