Jonathan da Buhari sun gana a Aso Rock

Image caption Shugaba Jonathan da Janar Buhari

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan da zababben shugaban kasar, Janar Muhammadu Buhari sun yi tattaunawa cikin sirri a fadar Aso Rock da ke Abuja.

Shugabannin biyu sun tattauna tsawon kasa da sa'a guda a cikin wani dakin taro da ke fadar.

Bayan kamalla tattaunawar, shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan ya bayyana wa manema labarai cewa sun tattauna a kan batutuwar da suka shafi kasar.

Jonathan ya kara da cewar "Za a tsayar da rana domin Buhari ya shigo fadar domin a nuna masa abubuwa a fadar."

Bayanai sun ce Janar Buhari ya isa fadar Aso Rock ne da misalin karfe uku na rana tare da shugaban jam'iyyar APC na kasa, John Oyegun da kuma Janar Abdulraman Dambazzau.

Wannan ne karo na biyu da Jonathan ya gana da Buhari tun bayan da aka zabi Janar din a matsayin shugaban kasa a cikin watan Maris.

A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da Janar Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban kasa a Nigeria.