EU za ta mayar da 'yan cirani kasashensu

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption 'Yan cirani a tekun bahar Rum

A karshen taron gaggawa da shugabannin kasashen Tarayyar Turai suka kammala a Brussels, an amince da a mayar da wasu 'yan cirani zuwa kasashensu na asali.

Shugaban majalisar kasashen turai, Donald Tusk, ya ce taron ya amince da ya mayar da wasu 'yan ciranin zuwa kasashensu na asali a inda wasu kuma za a ba su mafaka.

Taron ya kuma amince da yin karo-karon Yuro miliyan 120 domin daukar matakan hana kwararar 'yan cirani zuwa yankin turan.

Sannan Birtaniya tayi alkawarin jiragen ruwa da jirage masu saukar ungulu, a inda kasashen Jamus da Faransa da Belgium dukkanninsu suka yi alkawarin jiragen ruwa, domin yin sintiri a tekun.