India: An kama mutane 7 da laifin fyade

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sha yin zanga-zanga a kan cin zarafin da ake yi wa mata ta hanyar fyade a India.

'Yan sanda sun kama mutane 7 a birnin Mumbai na kasar Indiya, bisa zarginsu da laifin yi wa wata mata mai tallan kayan kawa fyade.

Matar mai shekara 29, ta ce abun ya faru ne bayan sun sami sabani da wani dillalin da ke harka da masu tallata kayan kawa inda ya so ya cuceta a kan kudi.

Matar ta ce bayan ta ki bayar da kudin, sai wadansu gungun mutane da suka hada da 'yan sanda suka kwace mata gwala-gwalanta tare da yi mata fyade.

Indiya dai tana shan suka a duniya saboda yadda ake cin zarafin mata a kasar.

Duk da cewa an gabatar da tsattsaurar doka, masu kare hakkin dan adam sun ce ba a cika gurfanar da laifuffukan fyade a gaban kotu ba a kasar.