Nijar: Ana kin amfani da gidan sauro

Hakkin mallakar hoto
Image caption Cutar Malaria na hallaka yara kusan dubu 500 a duk shekara a kasashen Afrika na kudu da hamadar Sahara

Matsalar kin kwana a gidan sauro mai magani na ci gaba da haddasa cutar zazzabin sauro ga al'umma a jahar Tawa ta Jamhuriyar Nijar.

Mutane da dama dai na cewa suna da gidan sauron amma ba sa amfani da shi, lamarin da hukumomi suka danganta da sakaci.

Jami'an kiwon lafiyar jahar ta Tawa sun ce ana ci gaba da samun karin masu cutar cizon sauron a sanadiyyar hakan .

An gano hakan ne yayin da aka shiga ranar yaki da cutar ta Malaria, ta duniya, a ranar Asabar din nan.