Yariman Saudiyya ya yi amai ya lashe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yarima Al-Waleed bin Talal.

Wani attajirin gidan sarautar Saudiyya ya goge wani furuci da ya wallafa a shafin Twitter na intanet, inda ya yi wa sojin Saudiyya matukan jirgin sama alkawarin cewa zai ba su motoci 100 domin hare-haren da suke kai wa a Yemen.

Yarima Al-Waleed bin Talal ya yi wa kowannen su alkawarin mota kirar Bentley.

Wasu 'yan Saudiyya sun yaba a kan wannan alkawari, suna masu cewa sojojin sun cancanci yabo, amma wasu 'yan kasar waje sun nuna bacin ransu game da wannan furuci inda suke cewa bai dace ba.