Nigeria ta janye jakadanta daga Afirka ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen Afirka da dama sun yi allawadai da hare hare akan baki a Afirka ta Kudu

Nigeria ta janye jakadanta daga Afirka ta Kudu bayan hare- haren da aka kaiwa baki a cikin kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen Nigeria a Abuja tace an nemi jakadan mai rikon kwarya Martin Cobham da kuma mataimakinsa Uche Ajulu Okeke da su koma Nigeria saboda a gana da su.

Akalla mutane bakwai aka kashe a hare haren da aka kaiwa baki 'yan Afirka a kasar, tun lokacin da Sarkin Zulu Goodwill Zwelithini ya ce 'yan kasashen waje su bar kasar

Tuni dai Sarkin ya bayyana cewa ba a yiwa kalaman nasa kyakyawar fahimta ba.

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudun ya yi allawadai da hare haren