Bam ya halaka sojojin Najeriya biyu

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Jos, babban birnin jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, sun ce wasu abubuwa sun fashe a barikin soja, inda suka kashe sojoji biyu.

Bayanai na cewa ba hari ne aka kai ba, fashewar ta faru ne a wani wurin ajiyar makamai yayin da sojoji ke kokarin kwashe tsaffin makaman da suka lalace.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito kakakin rundunar soji a Najeriya, Kanar Sani Usman, ya na cewa wasu tsaffin makamai ne suka fashe lokacin da ake kokarin kwashe su.

Abubuwan sun fashe ne a rundunar Igwa ta Uku da ke Rukuba, gab da birnin na Jos, inda aka samu hasara rayukan sojoji biyu, wani soja daya kuma ya samu raunuka.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar ta Filato, DSP Abuh Emmanuel, ya ce koda yake ya samu labarin faruwar lamarin, ba ya da cikakken bayani game da shi.

Karin bayani