'Yan Boko Haram sun sake kwace garin Marte

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram na ci gaba da kaddamar da hare harensu

Mayakan Boko Haram a Nigeria sun sake kwace garin Marte dake arewacin kasar, makonni bayan dakarun gwamnatin Najeriyar sun kwace shi.

Jami'an yankin sunce mayakan Boko Haram fiye da 2000 ne suka farma yankin sannan suka fatattaki Sojojin Nigeria.

Wannan dai shine karo na uku da mayakan na Boko Haram din ke karbe garin na Marte.

Rundunar sojin Nigeria dake samun goyan bayan kasashen dake da makwabtaka da Nigeriar sun kwace mahimman yankuna daga kungiyar Boko Haram a 'yan makonnin nan, amma masu ikirarin jihadin na cigaba da kaddamar da hare harensu