Ana sake zabe a Taraba, Imo da Abia

Hakkin mallakar hoto bbc

Jama'a a wasu sassan jihohin Taraba da Imo da kuma Abia sun fito kada kuri'a a wuraren da hukumar zaben Najeriya tace a sake zabe ranar Asabar din nan.

A ranar 11 ga wannan watan ne dai aka gudanar da zabukan gwamnonin jihohi a fadin kasar, amma wasu matsaloli suka hana kammala na jihohin Taraba da Imo da kuma Abian.

Rahotanni na cewa masu kada kuri'a sun fito a sassan da ake sake zaben, koda yake basu fito sosai ba a Jihar Imo.

Haka kuma, an jibge jami'an tsaro a wurare da dama na jihohin domin bai wa mutane damar kada kuri'a cikin lumana.

Alamu dai na nuna cewa zaben kujerar gwamnan na jihar Taraba dai yana cike da tarihi.

Idan 'yar takarar jam'iyyar APC, Sanata Aisha Alhassan, taci to za ta kasance mace ta farko da aka zaba a mukamin gwamna a kasar.

Idan kuwa dan takarar PDP, Ishaku Darius, ya samu nasara to jihar za ta kasance daya daga cikin jihohin da jam'iyyar PDP ba ta taba faduwa zabe ba.

Karin bayani