Okorocha, Ikpeazu sun lashe zaben Imo da Abia

Hakkin mallakar hoto no
Image caption Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo

A Najeriya hukumar zabe a jihar Imo ta bayyana Mista Rochas Okorocha na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar a zaben da aka sake gudanarwa.

Gwamna Okorocha ya lashe zaben a kananan hukumomi 20 cikin 23 a jihar, inda ya samu kuri'u dubu dari hudu da goma sha shida, da dari tara da casa'in da shida (416,996).

Babban abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Emeka Ihedioha ya samu kuri'u dubu dubu dari uku da ashirin, da dari bakwai da biyar (320,705).

A jihar Abia kuwa, hukumar zaben ta bayyana Mista Okezie Ikpeazu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka sake gudanar wa a wasu sassan jihar.

Mista Ikpeazu ya samu kuri'u dubudubu dari biyu da sittin da hudu da dari bakwai da goma sha uku (264,713) inda ya doke babban abokin karawarsa na jam'iyyar APGA, Mista Alex Otti wanda ya samu kuri'u dubu dari da tamanin da dari takwas da tamanin da biyu (180, 882).