'Yan Nepal na neman matsugunni

Hakkin mallakar hoto AP

Dubban jama'a a Nepal za su sake kwana a waje yayin da hanyoyin da aka rufe da kuma amon girgizar kasa suka kawo tsaiko a aikin dauki dangane da girgizar kasar da ta auku ranar Asabar.

Mutane fiye da 2500 ne suka rasu a sabilin girgizar kasar da amon da ya biyo bayanta.

Ma'aikatan agaji sun ce ana fuskatar matsalar rashin wutar lantarki da ruwan sha.

Gwamnati kuma na neman taimakon gina tantuna domin samar wa wadanda abin ya rutsa dasu matsugunni.

Ministan yada labarai na kasar ta Nepal, Minendra Rijal, ya shaida wa BBC cewa an tura tawagogi zuwa yankunan karkara domin taimakawa wajen tattara alkaluman mutanen da girgizar kasar ta shafa.

Yace: "Abin da muka yi shine daukar jiragen sama zuwa wadannan yankuna kuma da zarar sun isa can za su iya samun damar tattara yawan wadanda lamarin ya rutsa da su ko kuma wadanda suka jikata."

Karin bayani