Bulgeriya za ta hana bakin-haure shiga cikinta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An tsananta tsaro a kan iyaka tsakanin Bulgeriya da Turkiyya.

Bulgeriya za ta hana bakin-haure shiga cikinta

Kasar Bulgaria ta tura sojoji kan iyakarta da Turkiyya domin dakile matsalar shigar bakin hauren da ke biyowa ta haramtacciyar hanya daga Syria da Iraq.

Jami'an kasar na korafin a fakaice cewa hukumomin Turkiyya na turo musu 'yan gudun hijirar da suka yi musu yawa.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun sha sukar kasar ta Bulgaria saboda korar bakin haure da take yi da rashin ba su mafaka.

A makon jiya, Tarayyar Turai ta amince da matakan da aka dauka domin rage tsallakawar bakin haure tekun Bahar Rum -- duk da cewa wasu kasashen da ba su cikin tarayyar -- suna korafin cewa Tarayyar Turan ba ta kulawa da bukatunsu.