An gano rubabbun gawawwaki a Damasak

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram sun kwace garuruwa da dama a jihar Borno amma sojoji sun kwato mafi yawansu

Wani kwamitin gwamnatin jihar Borno ya gano daruruwan gawarwakin mutane da suka hada da mata da yara a garin Damasak a karshen makon da ya gabata.

Gwamna Kashim Shettima ne ya nada kwamitin domin tantance irin barnar da aka yi a garuruwa da kauyukan da aka kwato daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

A na dai tsammanin gawarwakin na mutanen da 'yan kungiyar Boko Haram suka kashe ne yayin da suke guduwa lokacin da ake gumurzu tsakanin 'yan kungiyar da sojojin Chadi.

Wata majiya ta tabbatarwa da BBC cewa an samu gawarwakin ne warwatse a kan tituna da cikin gidaje da manyan ramuka da kuma kogunan da suka kafe.

Kwamitin dai ya shafe gaba daya kwanakin karshen makon da ya wuce, wajen nemo gawarwakin tare da binnesu karkashin sa idon dakarun Chadi wadanda suka fatattaki masu tayar da kayar bayan daga Damasak makonni kadan da suka gabata.

Gwamnatin jihar ta ce za ta dauki nauyin sake gina garuruwan da samar da abubuwan bukatar rayuwa domin mazaunan garuruwan wadanda suka tarwatse su ji dadin sake zama a gidajensu.