Takaddama: Kotu ta yarda Ghana ta hako mai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yankin da ake takaddama tsakanin Ghana da Ivory Coast a kan hako man fetur

Kotun da ke sasanta kasashe a kan rikicin da ya shafi iyakokin teku ta bai wa kasar Ghana iznin hako mai a yankin da take takadaddama a kansa da kasar Ivory Coast.

Sai dai kuma kotun ta hana Ghanar gudanar da bincike domin gano sabbin rijiyoyin mai har sai an kamalla shari'ar.

Malam Abdul Fatau Akinyele, masani kan harakokin danyen man fetur da iskar Gas, ya yi shaida wa BBC cewa duk da wannan hukunci, akwai magana a gaba.

"Wannan abin farin ciki ne a wajen Ghana amma a iya cewa da sauran rina a kaba: kamar yadda kotun ta ce, har yanzu akwai sauran hakkin Ivory Coast a wannan bangare da Ghana ke hako man fetur da iskar gas," in ji Malam Akinyele.

Kotun dai ba ta yarda da bukatun da Ivory Coast ta gabatar ba, sai dai ta bai wa kasar dama ta bangare daya kacal.

Duk da hukuncin da kotun ta yanke a yanzu dai, rahotanni na cewa tsugune ba ta kare ba saboda akwai alamun sake duba shari'ar a can gaba.