An hana gyaran gira a Iran

Image caption Iran ta hana maza kwalliyar gira, da gyaran jiki, da zanen jiki wato tattoo.

A kasar Iran, an yi wa wanzamai gargadi a kan yi wa maza gyaran gira.

Kungiyar wanzaman kasar ta yi wa 'ya'yanta gargadin cewa gyaran gira ya saba ka'idar addinin Musulinci, wacce ita ce doka a kasar.

Dokar kuma ta yi hani da zanen kwalliyar jiki, wato Tatto.

Jami'an Iran sun yi kokarin kaddamar da dokar hana kwalliyar maza--irin su halawa da gyaran gashi na yayi mai kuma yanayi da kwalliyar nasara--amma ta kasa hana samarin kasar inda a kullum masu bin yayin nasarar karuwa suke yi.