Omar Al-Bashir ya sake lashe zaben Sudan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Omar Al-Bashir ya yi shekaru 26 yana mulkin Sudan

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya sake lashe zaben da aka gudanar a kasar da kusan kashi 95 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben, wanda 'yan adawa suka kaurace wa.

Shugaba Bashir -- wanda yake kan mulki tun shekaru 26 da suka gabata -- zai sake yin shekaru biyar yana mulkin kasar.

Al-Bashir ya yi alkawarin warware matsalolin da kasar ke fama da su da suka hada da tashe-tashen hankula da kuma rushewar tattalin arziki.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC tana neman Shugaba Bashir ruwa-a-jallo inda take tuhumarsa da kisan laifin kisan kare dangi.