Yemen: An gindaya sharuddan sulhu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan tawayen Houthi

Ministan harkokin wajen Yemen ya ce a shirye gwamnatin shugaba AbduRabbu Mansour Hadi take ta yi sulhu da 'yan tawayen Houthi bisa wasu sharudda.

Riyadh Yaseen ya ce tattaunawar za ta yiwu ne kadai idan 'yan tawayen Houthi suka mika manyan makaman su, sannan kuma suka ayyana cewa sun daina tawaye, da bi ta siyasa wajen cimma bukatunsu.

Mista Yaseen ya ce tayin da Ali Abdullah Saleh ya yi na tattaunawar, bayan barnar da ya haddasaba ba za a amince da shi ba.

Ministan wanda yake cikin jami'an gwamnati dake gudun hijira a Saudiya ya ce lugudan wuta da dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta suke yi, bai kare ba.

Mista Yaseen ya kuma kore yiwuwar yin sulhu da shugaban 'yan tawayen na Houthi Abdul Malik Al'Houthi da kuma tsohon shugaba Ali Abdullah Saleh da dan sa wadanda ake gani masu laifi ne.