Hukuncin kisa kan 'yan Nigeria a Indonesiya

Hakkin mallakar hoto JEWEL SAMADSONNY TUMBELAKASTRBAY ISMOYOMETRO TVSURYO WIBOWOAFPGetty Images
Image caption Kasashen sun bukaci Indonesiya ta yi wa mutanen afuwa

Kasar Indonesiya ta dukufa wajen zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutum tara da ta kama da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Kasar na fuskantar matsin-lambar daga kasashen duniya da ke neman ta hakura.

'Yan kasashen Australia da Brazil da Najeriya da Philipphines da kuma dan kasar ta Indonesiya na daga cikin wadanda za a zartar wa hukuncin kisan.

Iyalan fursunonin sun isa gidan yarin da ke wani tsibiri inda za a aiwatar da hukuncin kisan a kan 'yan uwansu.

Yawancin mutanen na cikin kaduwa, saboda bisa dukkan alamu, sun san wannan ce ganawar karshe da za su yi da su.

Kasar Faransa da Australia dai sun fito baro-baro sun yi Allah wadai da wannan mataki.