Mai shafin Wikileaks zai daukaka kara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mamallakin shafin Wikileaks Julian Assange

Kotun Koli a kasar Sweden ta bai wa mai shafin kwarmata bayanai na Wikileaks, Julian Assange damar daukaka kara kan yunkurin kama shi da a ke yi bisa zargin yin fyade.

Mista Assange ya samu fakewa a ofishin jakadancin Ecuador a London tun daga shekarar 2012 domin kada a mai da shi kasarsa.

Masu shigar da kara na gwamnati a Sweden suna son su yi mu shi tambayoyi game da zargin fayde a shekara ta 2010, zargin daya ce ba gaskiya bane.

Mista Assange ya ce idan aka tasa keyar shi zuwa Sweden, hakan zai sa Amurka ta tuhumeshi bisa kwarmata wasu bayanan sirrinta.

A watan Nuwamban bara wata kotun daukaka kara a Sweden ta yi watsi da bukatar da Mista Assange ya gabatar na daukaka karar.

Matakin kotun kolin ya zo ne bayan masu shigar da kara na gwamnatin Sweden sun sauya matsaya, inda suka amince su je London domin yiwa Mista Assange tambayoyi bayan sun shafe shekaru suna cewa sai dai ya koma Sweden.

Mista Assange ya musanta zargin da wasu mata biyu suka yi masa cewa ya yi musu fyade a shekarar 2010, inda ya ce suma matan an shirya da sune domin neman yadda za a mai da shi Sweden.