Kano: An dakatar da kamfanin da ke yin gada

Hakkin mallakar hoto Kano
Image caption Gwamnatin Kano ta ce tsautsayi ne ya sa gadar ta fadi.

Gwamnatin Kano da ke Najeriya ta umarci kamfanin da ke yin aikin gadar nan da ta fado ta kuma kashe mutane akalla bakwai ya biya diyya ga iyalan mutanen bayan ta dakatar da shi.

Wannan al'amari ya faru ne a kan titin marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam da ke unguwar Dorayi a ranar Lahadi da yamma.

Gwamnatin Jihar Kano ta kuma yi watsi da maganganun da ake yi cewa rashin nagarta ce ko kuma gaggawa suka sa bangaren gadar faduwa.

Kwamshinan ayyuka da gidaje na jihar ta Kano ya shaida wa BBC cewa tsautsayi ne kawai da ba ya wuce ranar sa ya sa gadar ta fadi.