An yi biris da dokar hana fita a Baltimore

Image caption Zanga zanga ta ci gaba cikin dare a Baltimore

Daruruwan masu zanga zanga a birnin Baltimore na Amurka sun ki aiki da dokar hana fita da daddare da aka sanya saboda tarzomar data biyo bayan mutuwar wani Ba'amurke bakar fata.

Masu zanga-zangar sun ci gaba da mamaye hanyoyi tare da jefa duwatsu a kan 'yan sanda da sauran jami'an tsaro da aka tura su tarwatsa su.

Kafin cikar lokacin da dokar za ta fara aiki, Magajiyar Garin Baltimore, Stephanie Rawlings Blake, ta gana da masu zanga-zangar inda ta roke su da su koma gidajensu.

Gwamnan jihar Maryland, Larry Hogan, wanda dan jam'iyyar Republican ne ya zargi jami'an tsaro da yin jinkiri kafin su dauki mataki.

Mista Hogan ya nuna cewa ba a dauki matakin daya kamata ba domin magance lamarin.

Zanga-zangar da ake yi sakamakon mutuwar mutumin bakar fata a hannun 'yan sanda, ta juye zuwa tarzoma a ranar Litinin, kuma ita ce mafi muni tun bayan kashe Marthin Luther King a 1968.