An toshe kafofin sadarwa a Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Daruruwan mutane ke zanga-zanga a Burundi domin nuna adawa ga tazarcen da shugaban kasar ke son yi

Hukumomi a Burundi sun rufe hanyoyin sada da zumunta na zamani, wadanda ake amfani da su wajen tattara kan mutane domin yin zanga-zangar nuna adawa ga shugaba Pierre Nkurunziza.

Daruruwan mutane sun mamaye titunan babban birnin kasar Bujumbura, a rana ta hudu da ake ta zanga-zangar adawa a kan shawarar da shugaban ya yanke ta neman ci gaba da mulki a karo na uku.

Wakiliyar BBC a kasar ta ga masu zanga-zangar kusa da yankin Musaga mai cike da mutane a birnin na Bujumbura, suna ihu tare da daga hannayensu domin su nuna wa 'yan sanda cewa ba sa dauke da makamai.

Sun shaida wa wakiliyar BBC cewa an hana su fita daga yankin ne kuma ba sa samun abinci a wajen.

Zanga-zangar dai ta fi yin kamari a unguwanni biyar na babban birnin kasar, Bujumbura, kuma an rufe kantuna da dama da ke tsakiyar birnin saboda zanga-zangar.