Ana binciken sojin Faransa kan cin zarafi

Dakarun Faransa a Jamhuriyar tsakiyar Afrika Hakkin mallakar hoto AFP

Faransa na gudanar da wani bincike zagayen farko game da zargin cewa sojojinta sun aikata fyade da luwadi a kan yara a Jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Zargin wani bangare ne na wani rahoton MDD wanda wata jaridar Birtaniya,the Guardian ta kwarmata.

Ma'aikatar tsaron kasar na bukatar a aiwatar da hukunci mai tsanani a kan sojojin da aka samu da laifi.

An gudanar da binciken ne bayan wasu takardu da wani babban jami'i a majalisar dinkin duniya ya mika wa jaridar ta Guardian a watan Yuli.

Sai dai kuma an dakatar da jami'in daga aiki bayan daya mika takardun sirrin.

Ya kuma ce yayi hakan ne saboda rashin aiwatar da wani abun azo a gani daga majalisar dinkin duniya kan zargin