An hana musulma shiga aji a Faransa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Faransa ta hana musulmai rufe jikinsu idan za su shiga aji.

Hukumomin wata makaranta a Faransa sun hana wata musulma daliba shiga aji saboda ta sa wani dogon sket baki.

Matakin dai yana cikin dokar hana sanya kayayyakin da za su nuna irin addinin da mutum ke yi, wacce aka kaddamar a shekarar 2004 a dukkan makarantun kasar.

Yarinyar 'yar shekaru 15 mai suna Sarah ta bi dokar makarantar, inda ta cire kallabin da ke kanta, sai dai ta ce ba ta yi tsammanin sanya dogon sket baki ya saba wa dokar ba.

Wasu malamai a kasar sun ce 'yan matan suna sanya dogayen bakeken sket ne domin nuna wa duniya cewa su musulmai ne.