Indonesia ta kashe masu fataucin kwayoyi 8

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban kasar Indonesia Joko Widodo

Kasar Indonesia ta zartas da kisa a kan wasu mutane 8 da aka samu da laifin fataucin miyagun kwayoyi a kasar, 7 daga cikin su 'yan kasashen waje.

Dakaru na musanman da suka kware da harbi ne suka kashe mutanen da daddare a tsibirin wani gidan kurkuku dake tsakiyar Java, duk da kiraye kitrayen da kasashen duniya suka yi a kan a yafe wa mutanen.

Shugaban kasar Joko Widodo ya sa an jinkirta kashe wata mata cikon ta tara, Mary Jane Veloso, inda ake binciken wata mata da ta ce ita ta yaudari Veloso ta shiga Indonesiya da jakar dake dauke kwayoyin.

Mutanen da aka kashe 'yan kasashen Australia da Brazil da Nigeriya da kuma Indonesia ne.

Prime Ministan Australia Tony Abbott ya yiwa jakadan kasar a Indonesia kiranye domin tattauna lamarin.

Gwamnatin Brazil ta ce kashe dan kasarta na biyu a Indonesia a tsakanin watanni hudu, zai yi mummunan tasiri akan huldar diplomasiyyar kasashen biyu.