An gano hanyar magance hatsarin motoci a Kenya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wata motar bas da ta tuntsure a kan hanyar filin jiragen sama a Mombasa.

Titunan Nairobi sun shahara wajen cunkoso ababen hawa.

Kananan motoci da bas-bas da tasi da babura da garken shanu suna jawo matsanancin cunkoso a titunan Nairobi, suna kuma bai wa mutanen da ke kokarin zuwa gida wahala.

Hanyoyin sufurin kasashen Afrika suna da matukar hadari kuma a Afrika ne aka fi samun yawan afkuwar hadura a duniya, inda take da kashi 16 cikin 100 na mace-macen da ake samu sanadiyar hatsarin ababen hawa, duk kuwa da cewa ita ce nahiyar da take da kaso biyu kacal cikin 100 na ababen hawar da ake da su a duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wata motar bas da ake kira Matatu wadda ake haya da ita a Nairobi

Matasa da dama suna hobbasa domin kawo mafita ga wannan masifa, inda suke kirkiro sabbin hanyoyin fasaha domin saukaka hanyoyin sufuri a biranen Afrika tare da inganta dokokin kiyaye afkuwar hadura.

'Kiran tasi a Nairobi'

A yayin da kasashen Afrika ke kokarin kaddamar da manhajar da za ta saukaka kiran 'yan tasi, tuni Kenya ta yi nisa wajen amfani da irin wannan fasaha saboda ficen da mutanen kasar suka yi wajen amfani da wayoyin hannu na komai da ruwanka.

A cewar shugabar wani kamfanin da ke ayyukan kiran tasi mai suna Easy Taxi, Lauren Gray, sabbin hanyoyin fasaha na taimaka wa kwarai wajen bunkasa harkokin zirga-zirgar motocin haya a Kenya.

Ms Gray ta ce hanyar fasahar za ta fi taimaka wa wajen sada mutane da ingantattun motoci masu cikakkiyar kariya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai tituna masu cunkoso da dama a babban birnin Kenya

Ms Gray ta kara da cewa amfani da fasahar wayoyin ta fi da gidanka na iya warware matsalar rashin ingantaccen hanyar sufuri tare da inganta tsaro, wanda ya zamo babban abin damuwa ga kasar Kenya.

"Abokan ciniki sun gano cewa idan suna bukatar motar haya da za ta kai su inda suke so, za a shirya hakan gabannin tafiyar za kuma a kira direbobi da dama domin a san wanda yake kusa da kuma wanda zai karbi kudi da sauki," in ji Ms Gray.

Hakkin mallakar hoto EASY TAXI
Image caption Kamfani saukaka hanyar sufuri na Nairobi ya ce amfani da fasaha na iya warware matsalar harkar sufurin Kenya

'Babur'

Ana amfani da fasahar wayar komai da ruwanka a wata hanyar sufurin ta Afrika wato babur, wanda aka fi sani da Boda-Boda a Kenya.

Alastair Sussock na daya daga cikin wadanda suka kirkiri kamfanin SafeBoda a Uganda, ya ce fasahar sufuri za ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban manyan birane a Afrika.

"Wannan fasaha za ta iya taimaka wa harkokin sufuri wajen kyautata wa abokan huldarsu kuma wannan shi ne abinda kamfanin SafeBoda ya fi maida hankali akai," in ji Alastair.

Image caption Babura na jawo cunkoso a titunan Kampala inda suke kutsa wa ta tsakanin motoci

Kamfanin SafeBoda yana amfani da manhajar Uber domin mutane su sami saukin kiran direbobin babur su kai su inda suke so.

Haka kuma, kamar yadda sunan yake, kamfanin SafeBoda ya yi nisa wajen bai wa direbobin kamfani horo wajen bayar da taimakon farko ga wadanda suka ji rauni da kiyaye dokokin tuki da kuma yadda ake kula da babura.

Mr Sussock ya kara da cewa amfani da fasahar sufuri zai taimaka wa bunkasar tattalin arzikin Afrika wajen samar da ayyukan yi.

"Babu wanda zai so ace fasaha ta maye gurbin mutane, abin da muke so shi ne samar da kasuwancin da zai rage yawan masu zaman banza a biranen Afrika.

Hakkin mallakar hoto SAFEBODA
Image caption Manhajar saukaka hanyar sufuri ta kamfanin SafeBoda

'Burin amfani da kayan lantarki'

A cewar Neil du Preez, mai kamfani Mellowcabs a Afrika ta kudu, mutane na bukatar su fara mayar da hankali kan hanyoyin amfani da fasaha domin rage irin tasirin da harkar sufuri ke yi a kan muhalli, musamman duba da yadda birane ke kara cika da mutane da kuma yadda cunkoso ke karuwa.

Mr Preez ya ce "Kamar yadda yawan mutane ke karuwa a birane da kuma hasashen da ake yi cewa kashi 70 cikin 100 na mutanen duniya zasu kasance mazauna birane a shekarar 2050, to ya zama wajibi a samu ingantattun hanyoyin sufuri masu aminci."

Hakkin mallakar hoto MELLOWCABS
Image caption Kamfanin Mellowcabs sun kera sabuwar tasi mai kafa uku mai amfani da lantarki

Tawagar kamfanin Mellowcabs suna kokarin aiwatar da fasahar lantarki a kowane bangare na tasi mai kafa uku, wadanda yanzu ake gwaji a kansu.

Ana iya kiran abin hawan ta hanyar amfani da manhajar wayar komai da ruwanka, wanda ke bai wa abokan hulda damar da zasu ga inda tasi din take da yadda zasu biya kudin da kuma adadin da zasu biya.

An kuma sanya musu fasahar da abokan hulda zasu ji dadin amfani da ita kamar su wajen cajin waya da wifi da abubuwan debe kewa duk a kokarin samar da ingantaccen fasahar sufuri a Afrika.